Al’ummar ƙauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara sun fitar da jerin sunayen mutane 85 da wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne suka sace a ranar Juma’a.
Duk da cewa jerin sunayen ba a nuna shekarun wadanda abin ya shafa ba, majiyoyi sun ce wadanda abin ya fi shafa sun hada da mata da kananan yara.
Da ta ke magana da Sashen Hausa na BBC kan harin, wata uwa da ta ce an sace Mata ƴa mai shekaru 15, ta bayyana damuwarta kan halin da yaran da ake garkuwa da su ke ciki.
“Muna cikin damuwa saboda ba mu san halin da yaranmu ke ciki ba,” in ji ta.
Wani uba kuma ya bayyana cewa babu wani gida da ke cikin ƙauyen yankin da lamarin bai shafa ba.
A halin da ake ciki, kokarin da wakilin DAILY NIGERIAN ya yi don jin martanin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ya ci tura, domin wayar a kashe ta ke yayin haɗa rahoton.
Haka shi ma Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Zamfara, Mamman Tsafe, bai dauki waya ko amsa sakon kar-ta-kwana da aka aika zuwa layinsa ba.