Wani ma’aikacin gwamnati Bala Musa mai shekaru 48 a duniya a ya maka fitacciyar jarumar Kannywood Hadiza Gabon a gaban wata kotun shari’a da ke Kaduna a ranar litinin bisa zargin kin aurensa.
Wanda ya shigar da karar ya shaidawa kotu cewa yana da alaka da jarumar kuma ta yi masa alkawarin aurensa.
“Ya zuwa yanzu na kashe mata N396,000. Duk lokacin da ta nemi kudi ina ba ta ba tare da bata lokaci ba, Saboda fatan za mu yi aure da ita”, Inji shi.
A nata bangaren, wanda ake kara wadda ya samu wakilcin lauyanta, Barr. Mubarak Kabir ya bayyana cewa wadda yake karewa bata da tabbaci Kan sahihancin da sammacin da aka Kai mata.
“Ta kuma kasa zuwa Gusau dake Zamfara inda nake zaune bayan na yi duk wani shiri na karbar bakuncinta,” in ji shi.
Daily News24 ta ruwaito cewa an fara sauraren karar ne a ranar 23 ga watan Mayu, amma wanda ake kara ba ta zuwa kotu bayan an kai karar.
Kabir ya roki kotun da ta kara masa lokaci domin gabatar da wadda yake karewa a kotu.
Alkalin kotun, Malam Rilwanu Kyaudai, ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Yuni.