BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Wanda mutane suka zaba ne zai gaje ni-Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alwashin cewa ba zai bari wani mahaluki ya kawo katsalanda ba a zabukan 2023 da ke tafe a Najeriya.

Buhari ya ce shugabancin da ba a gina shi kan turbar gaskiya ba, ba zai kawo wa kasa alfanu ba kamar yadda BBC ta ruwaito.

Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC da gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya jagoranta a fadarsa da ke Abuja.

Shugaban na Najeriyar ya kuma ce a karkashin shugabancinsa, zai ci gaba da mutunta ‘yan Najeriya ta hanyar tabbatar da cewa kuri’unsu sun yi tasiri saboda suna da yancin zabar shugabannin da suke so a dukkan matakai.

Leave a Reply