BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Tsohon Shugaban Kasar Kenya

Tsohon shugaban kasar Kenya Daniel Arap Moi ya mutu yana da shekara 95 a duniya.

Shugaban kasar ta Kenya Uhuru Kenyatta ya tabbatar da mutuwar tsohon shugaban kasar a wata sanarwa da ya fitar da asubahin Talata.

Mr Arap Moi ya dade yana jinya inda aka yi ta kwantar da shi a asibiti a lokuta daban-daban, kamar BBC ta ruwaito.

Ko a watan Nuwambar 2019 an yi ta yada jita-jitar mutuwarsa amma daga bisani mai magana da yawunsa Mista Lee Njiru ya musanta.

Kazalika ranar 29 ga watan Oktoba, 2019, wasu rahotanni sun ce an sanya wa Moi injin da ke taimaka masa yin numfashi a wani asibiti da ke birnin Nairobi bayan da aka kwantar da shi ranar 28 ga watan na Oktoba.

Shi ne shugaba na biyu da ya dade karagar mulki a Kenya tun bayan samun ‘yancin kanta a 1963, kuma ya shugabanci kasar tsawon shekara 24.

Leave a Reply