Kano Ayau Hausa, WASANNI

Tsohon dan wasan Sevilla Kanoute zai kuma gina masallaci

A lokacin da labari ya bulla a shekarar 2007 cewa Musulmin garin Seville za su rasa masallacinsu, tsohon dan wasan West ham da Tottenham Frediric Kanoute ne ya kawo masu dauki.

Kanoute ya bayar da tallafin dala 700,000, wanda hakan ya tabbatar da Fundacion Mezquita de Sevilla a matsayin masallaci ga dan kwallon da kuma daruruwan Musulmi a yankin.

Duk da cewa Kanoute ya gargadi abokan cinikinsa cewa bai yadda a bayyana cewa shi ne ya saya ba amma labarin ya bulla kwana guda da faruwar hakan.

Yanzu ma an ayyana wani makeken fili a garin Seville na kasar Spaniya a matsayin wajen da za a gina masallaci mai hawa uku wanda kuma zai hada da wajen ajiye motoci.

Wannan karon yana fatan tattara fan 250,000 ta hanyar gidauniyar da masallacin ke gudanarwa, wanda za a gina masallacin tun daga tushe irinsa na farko a cikin shakara 700.

Ma’ana dai za a gina masallaci na farko wanda aka kirkira don yin sallah a yankin cikin shekara 700.

An tattara rabin wannan kudin a makonnin farko na watan Ramadana da muke ciki.

“Na yi wasa na tsawon shekara bakwai a garin, kuma shi Musulmi duk sanda ya shiga bakon gari abu na farko shi ne ya nemi wajen da zai yi sallah,” Kanoute ya bayyana.

Ya kara da cewa: “Wurin da na je shi ne wannan masallacin na wucin-gadi. Na tarar da mutanen kirki wadanda mutanen garin ke kira ‘yan cirani, kamar yadda ake kiran akasarin Musulmi.

“Wadannan Turawa ne ‘yan Spaniya kuma ‘yan Andalus.”in ji shi kamar yadda BBC ya ruwaito.

Wasu ‘yan Spaniya ne Ibrahim Hernandez da Luqman Nieto suke taimaka wa Kanoute wajen ginin sabon masallacin, kuma har yanzu yana ji da garin Seville sosai a zuciyarsa.

Kanoute ya koma kungiyar Sevilla daga Tottenham ne a 2005. A shekara bakwai da suka biyo baya ya taka leda mafi muhimmanci a harkar kwallonsa.

Ya lashe kofin Uefa sau biyu, kofin Spanish Cup sau biyu da kuma European Super Cup hadi da Spanish Super Cup.

An kuma zabe shi gwarzon dan kwallon kafar Afirka na shekarar 2007.

Leave a Reply