WASANNI

Tsohon dan boksin ya rasu a hadarin mota

Rahotannin da ke fitowa daga kasar Jamus sun ce wani tsohon dan damben boksin mai suna Graciano Rochigiani wanda ake masa lakabi da “Rocky’ ya rasu a wani hadarin mota da ya rutsa da shi a kasar Italiya.

Kafar labarai ta UK Mirror da ke Ingila ta ruwaito a shekaranjiya Laraba cewa, tsohon dan boksin din ya gamu da ajalinsa ne a Italiya lokacin da ya kai wa budurwarsa wadda ta haifar masa ’ya’ya biyu ziyara.

A lokacin da yake cikin mota ne hadarin ya rutsa da shi, inda kafin a garzaya da shi asibiti, rai ya yi halinsa.

Graciano, wanda ya shahara a harkar damben boksin a Jamus, ya rasu yana da shekara 54.

Graciano ya lashe kyaututtuka a matakai daban-daban na damben boksin a ciki da wajen Jamus.

Marigayin ya yi wasannin dambe iri daban-daban har sau 48 inda ya samu nasara a wasanni 41 sannan ya yi canjaras a wasa daya yayin da ya samu rashin nasara a wasanni 6.

An ce duk nasarorin da ya samu a yayin damben, yana samun su ne tun a zagayen farko, in ban da a wasa daya da ya yi canjaras.

Tuni takwarorinsa da ke ciki da wajen Jamus suka aike da sakonnin ta’aziyyarsu ga hukumar shirya wasan damben boksin ta Jamus da gwamnatin kasar da kuma iyalan mamacin.

Leave a Reply