Kocin Tottenham, Jose Mourinho , ya kwatanta wasan da RB Leipzig ta doke su da ci 1-0 ranar Laraba da zuwa “fagen yaki da bindiga amma babu harsashi” a yayin da yake korafi kan jinyar da wasu manyan ‘yan wasansa ke yi.
Tottenham ta buga wasan ne ba tare da Harry Kane da Son Heung-min ba, kuma duk da cewa Erik Lamela da Tanguy Ndombele sun buga wasan amma dukkansu babu wanda ya murmure sosai.
Ya ce: “Muna cikin gagarumar matsala. Idan wannan wasan ne kawai, zan iya cewa babu matsala amma muna da gasar cin kofin FA da gasar Firimiya a gabanmu.”
Dan jaridar BT Sport, Des Kelly ne ya yi wa Mourinho tambayoyi cike da habaici, idan ya nusar da shi fafatawar da za su yi da Chelsea ranar Asabar mai zuwa.
Bayan wasan, za kuma su fafata da Wolves, Norwich da kuma Burnley ranar 10 ga watan Maris.
Leipzig sun yi wasan-kura da Tottenham inda Timo Werner ya zura kwallo, ko da yake Tottenham sun dan tagaza bayan an sanya Dele Alli da Gedson Fernandes domin maye gurbin Lamela da Ndombele.
Da aka tambaye shi ko yana ganin ‘ya wasansa sun taka rawar gani kuma sun nuna hakikanin kungiyar bayan sanya ‘yan wasan biyu, sai dan kasar ta Portugal ya ce: “Me kake nufi da hakikanin kungiyar?
“Ka san sau nawa Lamela ya yi atisaye a kungiyar nan? Ko sau daya bai yi ba. Ya buga wasan ne kai tsaye bayan ya dawo daga jinya…”
Ya kara da cewa: “Ba wai na damu ba ne kan kashin da muka sha da ci 1-0 – za mu iya zuwa gidansu mu ci su. Abin da ya fi damu na shi ne wadannan su ne ‘yan wasan da za su fafata a wasannin da za mu yi ko sau nawa ne.” kamar yadda BBC ya ruwaito.