Kano Ayau Hausa, Labarai

Taliban ta haramta wa ma’aikatan da ba su da gemu shiga ofis

Jami’an ma’aikatar kula da al’umma a Afghanistan na gudanar da bincike a gaban ofisoshin gwamnati domin duba ko tsawon gemun ma’aikata ya kai wanda hukuma ta umarta, kuma suna sanya kayayyaki kamar yadda Musulunci ya buƙata.

Ma’aikatar yaɗa Kyawawan Halaye da Hana Aikata Laifuka ta gargaɗi ma’aikatan gwamnati cewa za su iya rasa ayyukansu idan ba su mayar da hankali kan wadannan dokokin ba.

Wannan na cikin sabbin dokokin da ƴan Taliban suka kafa a ƴan makonnin nan.

An kulle makarantun sakandare na mata cikin sa’o’i bayan da daliban suka koma hutu a makon jiya.

An kuma hana mata yin tafiye-tafiye a jiragen sama na cikin gida ko masu zuwa kasashen waje ba tare da muharrami ba tare da hana cuɗanyar mata da maza a wuraren shaƙatawa, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Leave a Reply