BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Sulhu da ‘yan bindiga ne alheri-Yariman Bakura

Tsohon gwamman Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya ce zama teburin sulhu da yan bindiga ne hanyar da ta fi dacewa na kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya.

A cewarsa, irin zama teburin sulhu da gwamnatin tarayya ta yi da yan Neja Delta a kudancin Najeriya, idan aka bi irin tsarin, za a iya shawo kan matsalar tsaron a yankin arewa maso yammaci.

Ya ce yana kira ga sabbin manyan hafsashin tsaro da su zauna da ‘yan bindigar kamar yadda a baya aka zauna da ‘yan bindigar da suka addabi yankin Naija Delta a fara maganar sulhu da su.

”Ai ‘Yan Najeriya ne yawancinsu, an ce akwai mutanen waje, amma su ‘yan Najeriya ɗin a zauna da su a jawo hankalinsu a nuna musu yadda aka yi wa ‘yan Naija Delta, yadda aka sakar musu kudi bayan yin sulhun da su aka sakar musu kudi, suka fara sana’o’i da abin yi, su ma waɗanan nan a zauna da su a samar musu hanyar cin abinci”.

Yariman Bakuran ya ce idan hakan ta gagara to sai a bi su duk inda suke a ɗauki matakin da ya dace.

Dangane da sulhu da ‘yan bindigar, da wasu jihohin ƙasar suka yi yunƙurin yi a baya, wanda kuma bai yi nasara ba, Yariman Bakura ya ce ba a yi sulhun na gaskiya ba.

Sanata Yarima ya ce ”ba wai zama da su a yi musu alƙawari, sannan a watse ne sulhu ba, ni na bibiyi duk sulhun da aka yi da su a bayan, duka alƙawuran da aka yi musu an saɓa, domin ba za ka kira mutumin da talauci da jahilci suka sanya shi shiga daji sannan ka yi tunanin yin sulhu da shi ba tare da cika masa alƙawuran da ka ɗauka masa ba,” kamar yadda BBC ta kalato.

A filinmu na Gane mini Hanya na wannan makon Awwal Ahmad Janyau ya tattauna da tsohon gwamnan na Zamfara kan batutuwa da dama inda ya soma tsokaci kan yadda yake kallon kamun ludayin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Leave a Reply