Bataliya ta 202 ta rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun sake kubutar da wasu ‘yan matan Sakandiren Chibok guda biyu a jihar Borno.
Dakarun na Najeriya sun ce ‘yan matan biyu tare da ‘yayansu na asibitin soji inda ake duba lafiyarsu.
A wani sako da Sojojin suka wallafa a shafinsu na Tuwita sun ce sun ceto mata hudu ciki har da ‘yan matan Chibok biyu a lokacin wani samame da suka kaddamar
Sama da ‘yan matan Sakandiren Chibok 200 ne dai mayakan Boko Haram suka sace a shekarar 2014
To amma an kubutar da dama da cikinsu, sai dai har yanzu wasu na hannun mayakan na Boko Haram, kamar yadda BBC ta ruwaito.