Rundunar sojojin Najeriya a yau Alhamis ta yi nasarar dakile harin da ‘yan Boko Haram suka yi shirin kaiwa unguwar Gajiram a karamar hukumar Ngazai a jihar Borno.
Mataimakin Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojojin Opertaion Lafiya Dole, Kanal Onyema Nwachukw, ya ce sojojin sun kashe ‘yan Boko Haram da dama kuma sun kwato bindigogi yayin da suka yi yunkurin kai hari a garin a ranar Talata kamar yadda Aminiya ta ruwaito.