Labarai

Shugaba Buhari ya isa Maiduguri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Borno a ranar Laraba.

A lokacin ziyarar tasa, shugaban zai gabatar da jawabi ga dakarun kasar da ke yaki da kungiyar Boko Haram.

Ziyarar dai ta zo ne kwanaki kadan bayan ‘yan Boko Haram sun kai munanan hare-hare da suka yi sanadiyyar rasa rayukan sojojin kasar kimanin “100” a sansaninsu da ke jihar.

A tattaunawarsa da BBC mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya ce shugabani zai yi amfani da ziyarar wajen bude gagarumin taron ranar tunawa da sojoji wato “Army Day” da ake gudanarwa a kowacce shekara a kasar.

Leave a Reply