ADABI, Kano Ayau Hausa

Shin an canja sunan Kaduna zuwa Zazzau?

Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Uba Sani, ya bayyana rahoton da wasu kafafen yaɗa labarai suka wallafa kan batun ɗaukar nauyin ƙudirin sauya sunan jihar Kaduna zuwa jihar Zazzau a matsayin karya daga ramin wuta.
Sani ya musanta hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a yau Litinin. kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.
‘Sanatan ya nuna rashin jin dadinsa kan abin da ya suffanta a matsayin labarin ƙarya da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kudirin kafa jihar Zazzau, wanda ake zargin da haɗin gwiwar a Sanata Sulaiman Abdu Kwari a majalisar dattawa.
“Ta yaya mutane za su kai ga shirin dagula al’amuran jihar su da kuma ta’azzara matsalar rashin tsaro.
“Sanata Uba Sani ya samu cikakken goyon bayan jama’a kuma shi ne wanda za a kada wa kuri’a a zaben gwamna na 2023 a jihar Kaduna,” inji shi.
Sani wanda shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2023 a Kaduna, ya ce majalisar dattawan tarayyar Najeriya ta na hutu, inda ya tabbatar da cewa babu irin wannan kudiri da ke gaban majalisar.
Ya ce a kullum ana gabatar da bukatu na samar da jihohi a gaban kwamitin duba kundin tsarin mulki.

Leave a Reply