ADABI, Kano Ayau Hausa

ASUU ta tsawaita yajin aikinta da mako huɗu

Kungiyar Malaman Jami’o’i a Najeriya ta ASUU ta bayyana matakin tsawaita yajin aikin da take yi da mako hudu.

Dama ASUU ta shafe sama da watanni biyar tana yajin aikin bayan gaza cimma matsaya da gwamnatin Najeriya, yanzu kuma gashi ta kara wata daya.

Idan har aka shafe wasu makonni hudu ba a sasanta tsakanin gwamnati da ASUU ba, hakan na nufin ɗaliban jami’o’in sun shafe rabin shekara suna zaman jiran tsammani a gida.

Sanarwar da ASUU ta fitar na dauke da sa hannun Shugaban kungiyar Emmanuel Osodeke, an kuma fitar da ita ne bayan kammala wani zaman gaggaawa na jiga-jigan kungiyar ranar Lahadi a Abuja.

Hakama ASUU ta gode wa ƙungiyar Kwadago ta NLC, da sauran kungiyoyin da suka mara mata baya wurin yin zanga-zangar nuna goyon baya da nufin kawo karshen yajin aikin.

Kungiyar Malaman Jami’ar ta kara da cewa ta tsawaita yajin aikin ne da mako hudu, lura da cewa har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta nuna wata alama ta kawo karshen zaman daliban a gida ba.

Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu ne ASUU ta tsunduma yajin aiki, bisa zargin gwamnatin Najeriya da gaza cika alkawuran da ta dauka a yarjejeniyar da suka ƙulla, ciki har da batun inganta rayuwar malaman da kuma dambarwar shigar da kungiyar tsarin biyan albashi na IPPIS da gwamnatin ta fito da shi kamat muka kalato daga BBC.

Leave a Reply