Shugaban babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP, Iyorchia Ayu ya ce za su baiwa mutanen malam Ibrahim Shekarau da suka koma jam’iyyar mukamai lokacin nadin sabbin shugabannin jam’iyyar a jihar bayan rushe na da.
Shugaban na jam’iyyar PDP ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da BBC, inda ya ce za su baiwa mutanen Shekarau din mukamai ne sabo da a yanzu su ‘ya’yan jam’iyyar ne.
Ya kuma ce za a saka mutanen Ibrahim Shekarau ne a dukkan matakan shugabancin jam’iyyar a Kano kama daga jiha zuwa kananan hukumomi.
A ranar Litinin din nan ne, tsohon gwamnan na Kano ya sanar da ficewarsa a hukumance daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP saboda abin da ya kira “rashin adalci” da Rabiu Kwankwaso ya yi musu, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam’iyyar NNPP.