GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Sheikh Nuru Khalid ya samu wani Masallaci bayan an sallame shi daga Masallacin Apo

Tsohon babban limamin Masallacin Juma’a na unguwar ’yan majalisa da ke Apo a Abuja, Sheikh Nuru Khalid, ya ce ya samu sabon masallacin da zai ci gaba da jan sallah.

Sanarwar na zuwa ne a ranar da Kwamitin Masallacin na Apo ya sanar da sallamar shi gaba daya, bayan ya dakatar da shi tun da farko.

A karshen makon nan ne dai Kwamitin Masallacin, karkashin Sanata Sa’idu Dansadau ta fitar da sanarwar dakatar da malamin daga limancin saboda hudubarsa ta ranar Juma’a a kan matsalar tsaro.

To sai dai Sheikh Nuru ya ce tuni Kwamitin Gudanarwar sabon Masallacin Juma’ar da aka gina a unguwar ma’aikatan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya ba shi limanci a can.

Ya ce zai fara jagorantar sallah ne daga ranar Juma’a, takwas ga watan Afrilun 2022 mai zuwa.

Ya ce, “Da yardar Allah zan fara jan sallah a sabon masallacina ranar Juma’ar nan mai zuwa, saboda a matsayinmu na limamai, dole sai mutum ya samu wajen da zai rika limanci.

“Akwai sabon masallacin da muka gina a bayan unguwar CBN, ni ne zan rika jan sallah a can,” inji shi kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Malamin dai ya bayyana sallamar da aka yi masa daga masallacin na Apo a matsayin kaddararsa, saboda ya fadi gaskiya.

A yayin hudubar tasa dai, malamin ya kalubalanci gwamnati mai ci kan yadda ya ce ta gaza magance matsalar tsaron da ya addabi al’umma, musamman ma a kan harin jirgin kasan da aka kai a tsakanin Abuja zuwa Kaduna a makon da ya gabata.

Leave a Reply