Yaushe ne za a kawo karshen yajin aiki da kungiyar Malaman Jami’oi ASUU ke yi a Nijeriya, wace mafita kuma za a samu ta matsalar shiga yajin aikin da ake yi lokaci bayan lokaci? Wannna ita ce tambayar da kowa ke son ya ji amsar ta.
A ranar 5 ga watan Nuwanbar nan ne kungiyar Malaman ta shiga yajin aiki. Kungiyar ASUU din ta ce wannan yajin aikin ci gaba ne daga yajin aikin da ta shiga a watan Satumbar shekarar 2017 sakamakon rashin cika alkawarin yarjejeniyar da kungiyar ta yi da Gwamnati a shekara 2009 na ba Jami’oi naira biliyan dari biyu duk shekara domin inganta ayukkan makarantun da farfado da darajar su.
Shi dai wannan yajin aikin, an fara shi ne sakamakon rashin samun daidaito da cimma matsaya da kwamitin sulhu tsakanin Gwamnati da ASUU, wanda Dr. Wale ke jagoranta ya yi.
Kungiyar ASUU na ganin laifin Gwamnati na kin amfani da shawarar da ta ba ta, na hanyoyin da za su iya samar da kudin da za su iya biyan Jami’o’in. A dayan bangaren kuwa, Gwamnati na cewa, ba za ta iya jure biyan Jami’oin kudin da su ke bukata ba; a maimakon haka, Gwamnatin ta fito da sabon tsari na ba dalibai bashi a yayin da suke karatu, wanda za su biya idan sun kammala daga baya, wanda su kuma ASUU din ba su aminta da wannan ba.
Ina Matsayar Masu sulhunta tsakanin Gwamnati DA ASUU? Shugaban Kwamitin sulhun, Babaliki, ya ce, tare da hadin guiwar Babbar Majalisa mai kula da sha’anin ilimi ta kasa, kwamitin ya fitar da shawarar ba dalibai bashi.
“Babbar Majalisa mai kula da sha’anin ilimi ta kasa, ta cimma matsaya ta cewar, Gwamnatocin jihohi su fitar da tsari da za a dinga ba dalibai bashi. Haka kuma, majalisar na goyon bayan sabon tsari wanda bankuna za su baiwa dalibai bashi a yayin da su ke karatu, sai su biya bayan kammala karatun,” in ji Babalakin.
Babaliki, Farfesa Olufemi Bamiro, Farfesa Nimi Briggs, Farfesa Munzali Jibrin na daga cikin membobin kwamitin sulhun, sun bayyan cewar, Gwamnati ba za ta iya baiwa Jami’oi naira tiriliyan daya ba, saboda akwai wasu bangarorin da Gwmnati ke kula da su, ba Jami’oi kadai ba.
“Mu kaddara Gwamnati za ta ware naira tiriliyan daya duk shekara ga harkar ilimi, kaso 70 kenan na abun da gwamnati ta ware ga ayukkan raya kasa a shekarar 2007, to, gaskiya a namu tunanin, wannan ba zai yiyu ba duba ga cewa, akwai wasu bangarorin kamar bangaren lafiya, tsaro da wasu ayukkan ba za ta da kan iya tasowa da dole sai Gwamnati ta ware masu wani kaso su ma,” in ji kwamitin sulhun.
Shugaban Kwamitin sulhun, Babalakin, ya ce, kaso 22.5 ne kadai Gwamnati ta iya samarwa na abun da Jami’o’in ke bukata, to sai dai, ya bada shawarwarin wasu hanyoyin da za a iya bi wurin samar da wadatattu kudin
Har wa yau, Kwamitin sulhun ya bada wata shawarar ta magance matsalar, inda su ka ce, Gwamnati ta kara adadin tallafin (scholarship) da take ba dalibai zuwa kaso 30 a cikin dari, sai ya zama kason dalibai milyan 30 za su iya yi karatun su ta hanyar tallafin Gwmnati, ragowar kaso 70 din kuwa, su ne wadanda za a ba bashi Bankuna na naira miliyan daya duk shekara don gudanar da karatu da ayukkan makaranta.
“Matsayarmu ita ce, duk wanda ya samu damar karatu a jami’a (admission), amma kuma bai cika sharuddan samun tallafin Gwamnati ba (schorlaship), to, sai a bashi bashi na naira miliyan daya a kowace shekarar karatunsa. Dubu dari 7 daga cikin miliyan din, za su zama an biya mai kudin makaranta ne da su (registration), ragowar dubu dari ukun kuwa, sai a hannunta masa domin yin sauran zirga-zirg da ayyukkan makaranta.”
Kwamitin sun fitar da hanyar da dalibai za su biya bashin bayan kammala karatu, inda za su dinga biya kadan-kadan har su biya, wato kaso 10 na abun da mutum ya ke samu daga wurin aikin, sana’a ko kasuwanci sa. To sai dai kuma, akwai karin da mutum zai bayar yayin biyan bashi na kaso 5 (bashi da ruwa kenan (Intrest)”.
“Duk wanda ya cika sharudda, kuma ya ke da ra’ayi zai iya karbar bashi na Bankin. A yayin biya, mutum zai kara kudi , sai dai karin ba zai wuce kaso 5 ba ta yanda Bankuna ba za su durkushe ba”
“Za a tsara biyan bashin ne ta yanda dalibai ba za su fiye biyan kaso goma na daga abun da su ke samu ba,” in ji Kwamitin sulhun.
To abin tambaya a nan shi ne, yaya matsayar Kungiyar Malaman Jami’oi (ASUU) kan lamarin? A nasu bangaren kuwa, ASUU basu amince da shawarwarin Kwamitin ba. Da yake maida bayani kan shawarar Kwamitin, shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce, tsarin bashin banki ba zai taimaki dalibai ba, illa ma ya kara masu tsanani fiye da wanda su ke ciki, kuma tsarin bashin, ba komai ba ne illa hanyar kara kudi makaranta, in ji shi.
Shugaban ya kara da cewar, a lokutan baya, an taba jaraba wannan tsarin a Nijeriya, amma bai yi tasiri ba, yanzu ma, abun da za a fuskanta kenan ko da a ce an yi tsarin ne. Farfesan ya bayyan damuwarsa wurin biyan bashin, ind ya yi nuni da cewar, matsalar rashin aikin yi da ake fama da ita kan iya kawo cikas ga daliban wurin biyan bashin bayan kammala karatun.
“ASUU ba ta yarda da wannan tsarin bashin Bankin ba. An jaraba wannan tsarin tsawon shekara 7, daga shekarar 1993 zuwa 2001, amma ba a cimma nasara ba saboda matsalar cin hanci da rashawa, da kuma gazawar Gwamnati wurin yin abun da ya kamata, hakan ya tilasta ma wasu Bankunan rufewa,” in ji shi.
Da ya ke maida martani ga Bakaliki na Kwamitin sulhu, Farfesa Ogunyemi ya ce, tsarin bashin Bankin zai kara tsadar karatu da kuma kudin makaranta, ba kamar yanda kwamitin sulhu ke nunawa ba.
“Mun ji shugaban Kwamitin sulhu na cewa ba suna kokarin kara kudi makaranta ba ne. To, tambaya: cewa za su ba dalibai bashin miliyan daya, dubu dari 7 daga cikin kudin kuma kudin makaranta, wannna minene? Ba karin kudin makaranta ba ne da tsadar karatu?”
“Mu a wurin mu, wannan ba hanya mai bullewa ba ce; tarko ne kawai, su na neman kawo tsarin da idan an fara za a sha wahala kafin a daina, Bankuna za su karaya. Lalle wannan tarko ne ga dalibai, kuma kar su yarda su fada. Shin akwai ayukkan da ma za su yi ne idan har sun kammala karatun da har za su iya biyan bashin bayan kammala karatun?
“Idan da har Gwmnati za ta dabbaka tsarin da aka fitar na samar da kudi, wanda Kwamitin masana na kasa da ya hada da Babban ma’aji na kasa, Hukumar ma’aikatar ilimi ta kasa, Hukumar Makarantun Jami’oi ta kasa tare da ASUU su ka fitar, to da Jami’o’i sun samu isassun kudaden da ya dace”, in ji shugaban ASUU.
Ya cigaba da cewa, “Daga cikin shawarwari da muka ba Kwamitin sulhun, mun fada masu hanyoyin da Gwamnati za ta iya bi wurin samar da isassun kudi ga harkar ilimi. Mun kuma fada masu su dakile hanyoyin cin hanci
“Akwai wasu Hukumomi da Ma’aikatu da za a iya rage abun da ake basu zuwa ga harkar ilimi. Wadannan hukumomin da Ma’aikatun na da rarar kudin da basu a cikin kasafi ma, rara ce kawai, kasafin kudin su ma ba a bayyanawa, kawai su ke yin ‘kashe- mu-raba’ a tsakanin su. Misali, kamar Babban Bankin Nijeiya CBN, Ma’aikatar man fetur ta kasa NNPC, Hukumar NDIC da ta NIPOST, wacce aka kiyasta ta samu biliyan 5 daga kudin sitanfi kawai. Ammm Gwamnati ta ki ta yi komai a kai. Me zai hana Gwamnati ta ki dabbaka abubuwanda muka fitar a cikin rahoton da muka ba ta alhalin ta ce za ta yi?”, ya tambaya.
Da aka tamabayi Farfesa Ogunyemi me ya sa Jami’oin Nijeriya ba sa samar wa da kansu kudi ta hanyar bincike da nazari kamar yanda wasu Jami’oin ke yi a duniya?, sai ya ce, saboda rashi wadatattun kudi ne da makarantu za su iya amfani da su ne wurin gudanr da bincke da nazarin.
“Su wadancan Jami’o’in da ka ke magana, ta hanyar bincike da nazari ne su ke samun kudi, ba wai ta hanyar sayar da ‘pure water’ ba, ko sayar da biredi da fanke ba, wannan ba irin kalar kasuwancin da ya dace da Jami’oi ba kenan. Kafin mu iya kai ga wancan matakin, dole sai Gwamnati ta fara yin abun da ya kamata ta hanyar ware kudin da ya kamata ga Jami’o’i. Je ka gani a dakin karatu, za ka samu ba wadatattun littafai, haka ma dakin gwaje-gwaje za ka samu ba kayan aikin isassu,” in ji Farfesan
Farfesan ya kara dacewar, ba wai matsalar Malamai ba ne ke sa haka, a’a yanayin kula da harkar ilimi ne ke janyowa, amma akwai kwararru kuma masana a Nijeriya.
“Muna da kwararru a Nijeriya, shi ya sa za ka ga Malaman Nijeriya, idan sun je kasashen waje karatu suna samun nasara. Mu a nan yanayin sai a hankali, saboda rashin kayan aiki a fagen gwaje-gwaje, sai dai ma ko fagen karance-karance dama dama kenan.”
Da ace Gwamnati na amfani da masana wurin gudanar da ayukkan kwangila, to da duk da matsalar kudi, da Jami’oi sun iya samar da wani abu da kan su, inji Farfesan.
“Muna da kwararru masana ga duk kan ayukkan da Gwamnati za ta gudanar, amma ba sa amfani da mu saboda sun san, Malaman Jami’oi ba za su din ga basu na goro ba daga kudin kwangila ba kamar yanda su ke so.”
Farfesa Ogunyemi, ya ce, sun nemi Gwamnati da ta basu ragowar kayayyakin da ke Legas, wanda aka yi amfani da su lokaci da Legas ta ke babbar birnin Nijeriya yanzu kuma ba a amfani da su, domin su mallake su su samu kudin gudanrwa na Jami’oi, amma Gwamnati ta ki.
Da ace sun yi shiru da fafutukar su sun kyale kamar yanda malaman ‘primary\ da ‘secondry’ su ka yi, to da yanzu,halin da jami’oi su ke ciki a Nijeriya ya wuce yanda yake yandzu, inji Farfesa Ogunyemi.
“Muna yin wannan ne sabod nan gaba, makomar dalibai mu ke dubawa, saboda har nan gaba Jami’oi su wanzu. Da ace mun yi shiru mun kyale kamar sauran malaman kananan makarantu, to da yanzu yanayin da ake ciki ya wuce wannan.”
Yaushe ne za a kawo karshen wannan Takaddamar ta Yajin aiki tsakanin Gwamnati da ASUU, wannan ita ce tambayar da dalibai da yawa ke yi.
Wata dalibar Jami’ar Olabisi Onabanjo da ke Ogun, ta ce, bata ganin akwai wani abun alfano da wannan yajin aikin zai iya haifarwa, a cewar ta, su yi gaggawar samar da mafita don kawo karshen yajin aikin.
“Yajin aikin nan ya na cin lokacin mu ne kawai. Ya kamat in ga malamin da ke duba ni a binciken da na ken a kammala makaranta a wannna satin, amman haka bai samu ba sakamakon yajin aikin da ake.”
“Ba wani alfanu da muke gani ko da an ba Malaman kudin. Dakin kwamfutoci na amfani da ake ginawa tun lokcin da na fara makalarantar nan, shekara 4 kenan, har yanzu ba su gama shi ba”, in ji shi.
A halin yanzu dai ‘Yan Nijeriya sun zuba ido domin ganin yadda za ta kaya a tsakanin Gwamnati da ASUU a yayin da daliban da ke karatu a jami’o’in kuma aka jefa su cikin rashin tabbas.