Sarkin Zurmi, na Jihar Zamfara Alhaji Abubakar Atiku da aka tsige kwanakin baya ya rasu.
Sarkin ya rasu ne a Dubai bayan fama da matsanancin rashin lafiya.
Idan ba a manta ba, a 27 ga Afrilu ne Gwamnan Jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle ya dakatar da sarkin bisa zarginsa da taimakon harkokin ta’addanci a jihar.
Sarkin ya rasu ne a ranar Lahadi, kuma tuni aka fara shirye-shiryen dawo da gawarsa domin mata sutura.