BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Sarauniyar Ingila na fama da rashin lafiya mai zafi

Akwai damuwa a Fadar Sarauniyar Ingila, yayin da aka sanya Sarauniya Elizabeth ta II ƙarƙashin kulawa ta musamman bayan da likitocints su ka bayyana damuwarsu game da lafiyarta.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun masarautar ya fitar, likitocinta sun nuna damuwa da yanayin lafiyarta.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Bayan karin bincike da aka yi a safiyar yau, likitocin Sarauniya sun damu da lafiyar Mai Martaba kuma sun ba da shawarar ta ci gaba da kula da lafiyarta. Sarauniyar ta kasance cikin yanayin sauki kuma sanye da kayan ta na sarauta,” in ji sanarwar kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.

A cewar CNN, magadan Sarauniyar Yarima Charles na Wales da Yarima Williams na Cambridge sun yi tattaki don ziyartar kakarsu da ke fama da rashin lafiya.

Ita ma sabuwar firaministan na Burtaniya ya fitar da sanarwa.

Truss ya ce, “Duk kasar za ta damu matuka da labarin da aka samu daga fadar Buckingham a wannan lokacin na cin abincin rana,” in ji Truss, ta kara da cewa, “Tunanina – da tunanin mutane a duk fadin Burtaniya – suna tare da Mai Martaba Sarauniya da danginta a wannan lokacin. ” In ji sanarwar.

Leave a Reply