Al’ajabi, Kano Ayau Hausa

Sanyi ya kashe mutum 17 a Japan

Jami’ai a ƙasar Japan sun ce sakamakon yawaitar saukar dusar ƙanƙara a manyan biranen ƙasar ya yi sanadin mutuwar mutum 17 gommai suka jikkata, cikin kwana 10, yayin da dubban gidaje ke fama da rashin wutar lantarki.

Mafi yawan yankunan yammaci da gundumar Hakkaido da ke arewacin ƙasar na fuskantar yawaitar saukar dusar ƙanƙara a ‘yan kwanakin nan.

Kafar yaɗa labaran ƙasar ta ruwaito cewa akan samu yawan dusar kankara na kusan tsayin mita ɗaya a kowacce rana a wasu garuruwan gundumar Yamagata da ke arewa maso gabashin ƙasar, kamar yadda muka kalato daga BBC.

Hukumar kula da yanayi ta ƙasar ta gargaɗi mazauna yankunan da lamarin ya fi ƙamari da su kauce wa yin tafiye-tafiye bayan da ƙananan motoci suka yi ta maƙalewa cikin dusar ƙanƙara a kan wasu titunan ƙasar.

Leave a Reply