BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Sai mun sace Buhari da El-Rufai- ‘Yan bindigar jirgin kasa

Yan bindiga sun yi barazanar sace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a wani sabon bidiyo da suka fitar.

A sabon bidiyo da Aminiya ta gani, ’yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjoji sama da 60 a wani jirgin kasa da ke jigila tsakanin Abuja da Kaduna tun a ranar 28 ga watan Maris, sun yi barazanar sacewa da kashe Shugaba Buhari da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
A cikin bidiyon, ’yan ta’addan sun kuma yi bugun kirjin cewa za su ruguza kasar nan, sannan za su kashe wasu daga cikin fasinjojin da ke hannunsu su kuma sayar da sauran.

Daya daga cikin ‘yan ta’addan ya yi barazanar cewa, idan har gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba, to za su mayar da yankin tamkar mahauta.

Daya daga cikin ‘yan ta’addan ya yi barazanar cewa, idan har gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba, to za su mayar da yankin tamkar mahauta.

“Wannan shi ne sakonmu ga gwamnatin Najeriya kuma kamar yadda kuka ga wadannan mutane a nan, da yardar Allah za ku ga shugabanninku; Sanatoci da gwamnoninku za su zo gabanmu.

“Wadannan da kuke gani a nan za mu rike wasu a matsayin bayi mu sayar da su kamar yadda jagoranmu ya fada muku a baya,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa a cikin harshen Hausa: “Kamar yadda aka sayar da ’yan matan Chibok, za mu sayar da wadannan a matsayin bayi.

“Idan ba ku biya mana bukatunmu ba, za mu kashe wadanda muke da bukata mu sayar da sauran. Da yardar Allah, El-Rufai da Buhari za su shigo hannunmu.”

Leave a Reply