Uncategorized

Safara’u da Shuhura: Waiwaye akan tasirin Arewa24

Daga Ibrahiym A. El-Caleel

Malamai suka ce ita neman shuhura tana daga cikin cututtukan da ke kama zuciya. Kuma duk wanda ta kama shi, to zata mishi illa ne cikin addininsa.

Shi yasa ɗaya daga cikin Malamai, limami a Zuhudu, Imam Bishr bnul Hārith, wanda aka fi sani da Bishru Al-Hāfiy (Bishru mai yawo ba takalma), yace:

‎ما أعلم أحد أحب أن يُعرف إلا ذهب دينه وافتضح

“Ni dai ban san wani mutumin da yake son mutane su san shi ba, face sai ya rasa addininsa, sannan kuma asirinsa ya tonu.”

– Hilyatul Awliya na Abu-Nu’aym 3/94

A nan, Malam Bishru yana magana ne akan mutanen da suke amfani da ayyukan addini wajen neman su shahara, a sansu. Shine yace duk waɗanda ya sani sun yi haka, to sai da suka rasa addinin su; wato suka tarewa riya, sannan zaka same su da ƙarya, ko yaudara, ko cin amana. Sannan a ƙarshen al’amari, sai Allah ya tona asirin su. Ayyukansu marasa kyau na sirri, sai suyi ta ɓullowa a hankali a hankali.

To me kake tsammani kenan zai faru da duk wanda zai nemi shuhura da abin duniya!? Ai nashi lamarin sai ya fi zama watsattse.

Ba komai ne ya kai Safara’u wannan matsayi ba in banda son shuhra. Kuma ba ita kaɗai bace. Akwai matasa maza da mata a Arewacin Najeriya waɗanda son shuhra ta halaka, ko kuma zata halaka nan gaba. Amma ga bayani akan abinda nake nufi:

Tashar nan ta Arewa24 da ake ɗaukan lamarin ta da wasa, itace ummul-khaba’ithin da zata cigaba da kyankyashe Safara’o’i daga cikin al’ummar nan tamu.

A can baya, idan yaro ko yarinya suka taso da wannan ɗabi’a ta son waƙe-waƙe da raye-raye da gama-garin sharholiya, to babu wanda zai ji labarinsu. Babu wata shuhra da zasu samu. Dole bayan wani ɗan lokaci lamarin nasu ya watse. Idan ma bai watse ba, to iyakar su gidajen gala da kulob ɗinsu na ƴan nanaye. A unguwannin su kuwa kyamar su ake, saboda an san abinda suke yi ya saɓawa addini da al’adar mutanen kwarai. Ba’a ɗaukar su da daraja sam, balle wani yayi fatan zama kamar su.

Amma tunda Arewa24 ta zo, sai suka ce asali ma sun kafa tashar ne don raya irin waɗannan ayyukan assha. Wai suna fatan tashar ta ɗauke hankulan matasa daga mugayen ayyuka irin shaye-shaye da tsattsauran ra’ayin dake sabbaba ta’addanci. Sai suka janyo matasa a jika; aka fara ganin baƙonnin fuskoki a cikin drama, waƙoƙi da sauran abubuwa dai. Mutanen da asali ake kyamar su a cikin al’umma, sai Arewa24 ta maida su wasu masu martaba (VIPs).

Saboda haka, yanzu duk yaron da ya taso da himmar drama ko waƙa ko wani shashancin, Arewa24 zasu janyo shi a haska shi a talabijin. Daga nan an ‘taimake’ shi mutane su san shi. Don haka manyan maɓarnata zasu ganshi, idan ‘basirar’ sa ya birge su, sai su janyo shi a jika. Daga nan a ƙara ɗaura shi akan harkar sosai. Har sai ya wayi gari ya zama irin Safara’u! Wato shima idanun sa sun kafe; baya jin kunyar ya tsaya a gaban kyamara yayi komai. Baya shakkar faɗin kowace irin magana idan ana hira da shi. Bashi da wani abu da yake kallo a matsayin wai abin kunya ne!

Ana haska yaran nan mawaƙa a talabijin duniya ta gansu. Kuma yanzu suna shahara, suna tara dubbannin mabiya a shafukan su na social media. To ai aikin gama ya gama! Yadda yara suke da son shuhra, ka ga ba zasu yi wasa da wannan dama ba. Haka zasu cigaba da dagewa, suna ƙoƙari ko ta halin ƙaƙa, suma dai a haska su a talabijin. Har daga garuruwa irin Damaturu fa yanzu ana samun mawaƙan nan da ake haskawa. Ka ga ai an yaƙe mu sosai kuwa.

To ina mafita?!

Kimanin shekara ɗaya kenan da nayi wani rubutu akan tashar Arewa24, lokacin da na ji wasu mutane suna ta kiran gwamnati cewa ta dakatar da tashar. Sai na lura waɗannan mutane suna buƙatar sake nazari akan lamarin.

Wannan ba fa yaƙin ƙarfin tuwo bane. Yaƙi ne na kwakwalwa (intellectual war, الغزو الفكري). Don haka idan kace zaka kawo ƙarfin tuwo, to ina tabbatar maka kawai ɓata lokacin ka kake yi. Na bada labari tun a wancan rubutun nawa cewa, tun daga Ƙasar Urdun (Jordan) ake watsa shirye-shiryen wannan tashar. Don haka, tashar nan fa ba za’a rufe ta ba! Ina so ka sa wannan a ranka.

Abinda kai zaka iya yi shine: Kai ka rufe tashar a gidan ka. Idan kuma ba zaka iya ba, to ya kake tunanin ita gwamnati zata iya rufewa a duk Najeriya? Yadda gwamnati ke da iko a ƙasar, haka kai ma kake da iko a gidanka.

Kawai mafita shine: Iyaye, billahil azheem, kuna da babban aiki a gaban ku. Dole ne ku sanya idanu sosai akan tarbiyyar yaran ku, tun suna yara, kuma musamman idan suka fara tasowar balaga. Daga nan ne suke fanɗarewa. Kada ku taɓa tunanin wai akwai ranar da ake gama tarbiyyar yaro. Shi ɗa kana fara mishi tarbiyya ne tun yana tsumma. Ba ka denawa sai ranar da aka saka shi a lakafani, aka birne shi, ka juyo ka dawo gida. To a ranar ne ka gama mishi tarbiyya! Amma in har yana da rai, wajibin ka ne ka cigaba da mishi tarbiyya gameda halaye nagari, da kuma halayen banza. Dole ne wannan akan ku, Baba da Mama.

Abu na biyu: yadda ka sanyawa ɗanka, ko ƴarka so da sanin darajar karatun boko, to dole ka sanya musu son da sanin darajar karatun addini. Tun daga yarinta, ka tarbiyyantar da su akan imani da Allah, da cewa Allah fa Ya san abinda suke yi, kuma tabbas akwai azaba da ni’imah a cikin ƙabari, da kuma a lahira. Don haka su bi Allah, su nisanci Sheɗan da ayyukan sa.

Abu na uku: Ya ku iyaye, zama bai same ku ba! Dole ku dage da addu’a ga ƴaƴan ku. Safe, rana da dare! Kuma ku saba da sanya musu albarka. Ku guji tsine mu, da allawadai da su, da hantarar su haka kawai. Bakunan ku yana da babban tasiri akan ƴaƴanku. Ku lazimci amfani da bakunan ku wajen musu addu’a da fatan alherin duniya da na lahira.

Sheɗan ba zai zubar da makaman yaƙin sa ba. Sheɗan ya faɗawa baban mu Annabi Adamu (A.S); ya kuma nemi Allah Ya ɗaga masa ƙafa zuwa Ranar Lahira; sannan ya sha alwashi cewa sai ya halaka zurriyar Annabi Adam, in banda waɗanda Allah ya kare. Don haka mu dage kada mu zama cikin waɗanda Sheɗan da rundinarsa za suyi nasara akan mu, su halakar.

Arewa24 ɗaya ce kawai. Kuma kada kayi tunanin wai shikenan ita kaɗai zata zauna. A’a. Ta yiwu akwai wasu ma suna nan tafe nan kusa, ko nan gaba. Duk zasu yi amfani ne da irin yadda ɗan Adam ke son mutane su san shi, shikenan su yaudari yara, su ɗauka su akan hanyar salwantar da addinin su. Kai dai kayi wajibin ka kawai wajen tarbiyya haɗe da addu’a.

Allah Ubangiji Ya kare mu daga sharrin Sheɗan da rundinar sa, Amin.

– Ibrahiym A. El-Caleel ne ta fara wallafa wannan rubutun a shafinsa na Facebook

Leave a Reply