GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Rayuwa ta ishe ni-Aminu Dantata

Hamshaƙin ɗan kasuwar nan da ke jihar Kano a arewacin Najeriya Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ya bayyana cewa a halin da ya ke ciki baya jin daɗin rayuwa babban burinsa da fatansa shi ne cikawa da imani.

Aminu Dantata mai kimanin shekaru 91 da haihuwa ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke karɓar baƙuncin ɗan takarar mataimakin shugaban Najeriya a jam’iyyar APC a gidansa da ke birnin Kano.

Ya ce a lokacin ƙuryciyarsa ya yi mu’amala da harkar kasuwanci da mutane masu yawan gaske wanda a yanzu abu ne mai wahala ya zayyano mutum goma da su ke raye.

Na yi yawon fatauci a dukkanin jihohin Najeriya inda na yi mu’amala da mutane da mafi yawansu abokan cinikayyata ne a waɗannan jihohi. Sai dai abin takaici shi ne a cikin jerin waɗanda mu ka haɗu abu ne mai wahala in zayyano mutum goma da su ke da rai”

Maganar gaskiya a halin yanzu ina jiran wa’adi ne domin bana jin daɗin rayuwa, burina in cika da kyau da imani” In ji Aminu Dantata kamar yadda muka kalato daga Labarai24.

Haka kuma hamshaƙin attajirin ya ƙara da cewa yana fatan duk wanda ya yi ba daidai ba ya yafe masa shi kuma duk wanda ya yi masa ba daidai ba ya yafe masa.

Leave a Reply