Farashin man fetur ya karye a defo-defo na Najeriya a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin ƙarin farashin man zuwa naira 700 a kan duk lita ɗaya cikin wannan wata na Yuli.
Ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya, IPMAN ta tabbatar da karyewar farashin, ta ce ana sayar da shi a kan naira ɗari huɗu da ɗoriya, saɓanin sama da naira ɗari biyar a kan duk lita ɗaya.
Shugaban ƙungiyar reshen arewacin Najeriya, Bashir Ahmed Danmalam ya shaida wa BBC cewa farashin ya karye ne saboda ƙarancin masu saye, kuma za a samu rangwamen har a gidajen mai.
Danmalam ya ce tun kafin tafiya hutun sallah, farashin man fetur ɗin ya fara sauka.
“A yanzu haka, man fetur a defo-defo ɗin da ke Lagos da Warri da Calabar, an samu sauƙi domin ana (samun sa a kan) ƙasa da naira ɗari huɗu”.
Jami’in na IPMAN ya ce farashin man zai yi ƙasa a kwanaki masu zuwa a sassa daban-daban na Najeriya.
“A makon da muke ciki farashin zai yi ƙasa, sannan kuma ya kamata a san cewa yawan masu sayen man fetur ma ya ragu, ba kowa ne yake da kuɗin da zai iya sayen mai yanzu ba”.
‘Za a fara ganin sauyi’
Shugaban ƙungiyar ta IPMAN a arewacin Najeriya ya danganta faɗuwar farashin man fetur ɗin a kan wasu dalilai biyu da suka haɗar da rashin kuɗi da kuma damuna.
Ya ce da ma a al’ada idan damuna ta kankama, manoma ba sa bukatar su sayi mai, akwai kuma rashin kuɗi da kuma rashin amfani da man, don haka dole shi kansa farashin fetur ya karye.
Sai dai duk da cewa Bashir Dan-malan bai bayyana taƙamaiman lokacin da za a fara samun man fetur mai sauƙin a gidajen mai ba, amma ya ce nan ba da jimawa ba mutane za su fara gani.
Danmalam ya ce ana dab da ganin sauyi, saboda ba kowa yake da kuɗin da zai iya siyan mai yanzu ba.
Shugaban kungiyar IPMAN reshen arewacin Najeriya ya ce hasashen da suka yi tun farko a kan cewa farashin man fetur zai iya kai naira 600 zuwa 700 a lokacin bazara zai iya faruwa ne kawai idan aka fuskanci ƙarancin dala.