‘Yan Najeriya sun caccaki shahararren mawakin nan na shugaban kasa Muhammadu Buhari da manyan ‘yan siyasar Arewa, Daudu Kahutu Rarara, kan sabuwar wakar da ya yi na sukar gwamnati kan tsaro.
Mawaki Rarara ya yi kaurin suna wajen wakewa da yabon Buhari, kuma yana kan gaba cikin wadanda suka yi masa kamfen don ganin ya zarce a kan kujerarsa a 2019.
Saboda haka ne ma shugaban kasar ya nada shi a matsayin shugaban mawakarsa.
Sai dai kuma mutane da dama sun cika da mamaki a lokacin da suka wayi gari da wakarsa wacce ta bayyana a shafukan sada zumunta inda a ciki yake kalubalantar gwamnati a kan rashin baiwa al’ummar kasar cikakken tsaro.
Harma a cikin baitin wakar tasa ya bayyana cewa yan kadan ne ke yiwa gwamnatin Buhari uzuri a yanzu saboda ta gaza kare kasar, inda yace ana jin wai-wai a da amma ga shi abun ya bayyana a zahiri.
Tuni dai yan Najeriya suka fito suka yi sharhi kan lamarin, inda da dama ke ganin mawakin na kokarin samun wani tudun dafawa ne duba ga cewar wa’adin wannan gwamnati na gab da karewa.