Musulmin Kudu-maso-Gabas,a ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Da’awah ta Musulmin Igbo, za ta ƙaddamar da Alkur’ani mai tsarki da aka fassara da harshen Igbo a ranar Juma’a.
Da su ke zantawa da Daily Trust a yau Alhamis, wakilan ƙungiyar, ƙarƙashin jagorancin Muhammed Muritala Chukwuemeka, sun ce shi da tawagarsa sun yanke shawarar isar da saƙon Allah ga ‘yan’uwansa Igbo ta hanyar Alkur’anin da aka fassara da yaren na su.
A cewar rahoton, Chukwuemeka, dan asalin Ƙaramar Hukumar Orlu ta jihar Imo, ya bayyana addinin musulunci a matsayin addinin zaman lafiya da ya haramta kashe ɗan’adam, inda ya ƙara da cewa aikin fassarar ya ɗauki kusan shekaru biyar kafin ya kammala.
Ya yi kira ga ƴan Najeriya da su halarci taron ƙaddamar da bikin, wanda za a yi bayan sallar Juma’a a masallacin Ansar-ud-deen da ke Maitama, Abuja.
Chukwuemeka ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya masu kishin kasa da su tallafa wajen samar da littafi mai tsarki domin isar da saƙon Allah cikin lumana ga ’yan ƙabilar Igbo a Kudu-maso-Gabas da sauran sassan Najeriya.
“kasa da shekara biyar ba kafin na kammala fassarar. Muna kira ga ’yan Najeriya masu hannu da shuni da su taimaka wajen samar da littafi mai tsarki da yawa. A yanzu haka mun buga kwafi 500 kuma an riga an tura kwafi 100 zuwa Kudu maso Gabas,” inji shi kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.