Kano Ayau Hausa, Labarai

‘Yan sanda sun dakatar da Tashe a Kano

Bisa al’ada, idan azumin watan Ramadan yakai kwana 10, akwai al’adar Tashe da kuma kidan gwauro da ake gudanarwa a kasar Hausa, wanda a wannan shekarar hukumar yan sanda ta jihar Kano, tace babu bukatar hakan, kuma tayi gargadi mai zafi ga duk wanda ya fito ya aiwatar da hakan.
Nasara Radio (Amanar Talaka) ta rawaito cewa, kakakin hukumar reshen jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a yau, wanda yayi kira ga iyaye da su tabbatar basu bar ‘ya’yansu sun karya doka ba, domin kuwa duk wanda aka kama da karya doka, ba shakka doka zatayi aiki akan kowa.
Kiyawa wanda ya fitar da sanarwar a madadin kwamishinan yan sanda na jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, yace an dakatar da waccan al’ada ne ta Tashe saboda gudun kada bata gari suyi amfani da wannan dama domin ayyuka marasa kyau, musamman ‘yan daba, masu kwacen waya da kuma ‘yan shaye-shaye, kamar yadda Nasara Radio 98.5 FM ta ruwaito.

Leave a Reply