Fitacciyar jarumar Kannywood Rahamda Sadau ta kammala karatunta a wata Jami’ar kasar Cyprus.
Rahama ta wallafa a shafinta na Instagram cewa, “abin da kamar wuya, amma kuma mun kammala.”
Ita dai Rahama ta yi karatun ne a bangaren Human Resource Management a Jami’ar Eastern Mediterranean.