Kano Ayau Hausa, Siyasa

Peter Obi ya fice daga PDP, akwai alamar ya koma NNPP

Peter Obi na cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a Twitter a ranar Talata bayan ya fice daga talakarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan na Anambra ya fice PDP yana mai bayyana cewa ba zai iya ci gaba da tafiya a jam’iyyar ba.

Ya ce zai ci gaba da bayar da gudunmuwarsa wajen taimakawa Najeriya magance matsalolinta.

Peter Obi ɗan kasuwa ne wanda ya shiga jam’iyyar PDP a 2017.

Ya yi takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Atiku Abubakar a zaɓen 2019.

Babu dai wata manufa da ta fito kawo yanzu kan daliln ficewarsa daga takarar shugaban ƙasa da kuma inda ya dosa.

Amma a kwanakin baya ƴan Najeriya musamman a Twitter sun ta alaƙanta shi da tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP kamar yadda muka kalato daga BBC.

Leave a Reply