Kano Ayau Hausa, WASANNI

Pep Guardiola ya ce ba zai taba horar Manchester United da Real Madrid ba

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce ba zai taba karbar aikin horar da Manchester United ko Real Madrid ba.

Guardiola ya ce ya fi kaunar ya tafi hutu da ace ya koma Old Trafford.

Guardiola yana cikin sahun gaba aka yi tunanin zai gaji Sir Alex Ferguson amma kuma ya kulla yarjejeniya da Bayern Munich, lokacin da Ferguson ya yi ritaya a 2013.

Kocin ya ce matabarsa a City ya nuna cewa ba zai taba komawa United, koda kuwa ita ce kungiyar tilo da ta nemi shi.

“Idan har ban samu aiki wani wuri ba, zan kasance a Maldives,” in ji shi kamar yadda BBC ya ruwaito.

“Bayan horar da City, ba zan taba horar da United ba, kamar yadda ba zan taba horar da Madrid ba,” a cewar Guardiola, a yayin da yake magana kan ziyarar da zai kai Old Trafford a gasar lashe kofin Carabao wasan dab da karshe ranar Talata.

“Ba zan taba ba.”

Leave a Reply