BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Otel din da El-Rufai ya rusa ya zama Masallaci

Daga Ibrahim Adamu Datti

Tun kafin zuwan malam Nasir Elrufai Gwamna a Jihar Kaduna Ina daga cikin wadanda muke dinga gwagwarmaya domin a rufe wasu otel guda uku a cikin Unguwan mu wanda suka hada Mashi Guess IN,FMC da Lujuana Otels wanda duk mallakin wasu Iyyamurai ne, saboda suna kawo matsalar tsaro, lalata da matan aure da kananan yara sannan suna tsakiyar mutane, amma duk wani yunkuri namu ya ci tura.

Cikin ikon Allah, aka rubutawa Elrufai koke akan wadannan Otel din kuma ya yi bincike da kansa ya zo ya rushe su sannan ya soke takardun mallakar filayensu. Wannan Katafaren Masallacin da kuke gani daya ne daga cikin Otel otel din daya rushe, mutanen unguwa suka gina Masallaci da Islamiyya kuma yau ake bikin bude shi domin hada-hadar watan Ramadana.

Allah ya sakawa Malam Nasir Elrufai bisa wannan Namijin kokari Allah yakai lada ga mizani.

Leave a Reply