BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Osinbajo zai wakilci Buhari a jana’izar Sarauniya Elizabeth II

Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo zai wakilci Najeriya a jana’izar Sarauniyar Ingila da za a yi a ranar Litinin a Birtaniya, kamar yadda muka kalato daga BBC.

Mai taimamaka wa Farfesa Osinbajo kan harkokin watsa labarai Laolu Akande ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar inda ya ce mataimakin shugaban ƙasar zai bar Najeriya yau Asabar domin ya haɗu da iyalan Gidan Sarautar Birtaniya da Firaiministoci da shugabanin ƙasashen renon Ingila da sauran shugabannin duniya.

Farfesa Osinbajo na daga cikin manyan baƙin da Sarki Charles III zai karɓi baƙwancinsu a wani taro da za a yi a Fadar Buckingham gobe Lahadi.

Leave a Reply