Kano Ayau Hausa, Siyasa

Ofishin INEC ta Filato ta kone

An kona daya daga cikin ofishin hukumar zabe a Najeriya kwanaki shida kacal kafin gudanar da babban zabe a kasar.

Gobarar dai ta faru ne a ofishin hukumar a jihar Filato dake arewacin kasar inda muhimman kayayyakin zabe kamar akwatuna da takardun jefa kuri’a suka kone.

Mai magana da yawun hukumar ya bayyana kona ofishin a matsayin mayar da hannun agogo baya a bangaren shirye-shiryen zabe.

A wata sanarwa da hukumar zaben ta fitar ta bayyana cewa wannan ne karo na biyu da aka samu konewar ofishinta a cikin wannan watan, inda tayi kira ga jami’an tsaro a kasar da su kara matsa kaimi wajen ba ofisoshinsu tsaro.

Ana sa ran dai za a gudanar da babban zabe a kasar a ranar Asabar.

A ranar lahadi ne dai shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi gargadi a kan magudin zabe.

A wani bangaren kuma, shugaban ya koka a kan zargin da hukmar EFCC a kasar tayi na makudan kudaden da ake fitarwa ba bisa ka’ida ba domin siyan kuri’a.

Leave a Reply