BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ni ba dan bangar siyasa ba ne-Abba Gida-gida

Dan takarar gwamnan Kano karkashin jam’iyyar NNPP, Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida), yayi martani ga shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, bisa zarginsa da yayi akan haddasa rikicin daba a Unguwar Chiranci dake karamar hukumar Gwale.

Abba, ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, inda yace kowa yasan Abdullahi Abbas ya kafa tarihin ta’addacin siyasa a jihar Kano, duba da yadda yake umartar yara su farmaki mutane.

Sanarwa tace, gidan da ake magana akansa, ofishin jam’iyya ne, kamar yadda kowacce jam’iyya ke da ikon bude ofishi haka ita ma NNPP ta bude a Chiranci, kuma babu wani abu mai kama da dabanci ko shaye-shaye ko makamai a gidan.

Bature yace, Abdullahi Abbas yana kokarin nade Tabarmar kunya ne da hauka, yana so ya lullube laifinsa ga hukuma, don tsira daga tuhumar yan sanda ko sammacin kotu bisa ayyukan ta’addacin da yayi, musamman na baya bayan nan, wanda kuma hakan ba zai yiwu ba, inji shi kamar yadda muka kalato daga Nasara Radio.

Leave a Reply