Al’ajabi, Kano Ayau Hausa

NDLEA ta kama tsohon ɗan ƙwallon ƙafa kan safarar hodar ibilis

Hukumar NDLEA ta kama wani tsohon dan ƙwallon kafa, Emmanuel Okafor a filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Ikeja, bisa laifin safarar hodar iblis.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a yau Lahadi a Abuja, inda ya ce an kama Okafor ne a lokacin da ya taso daga Sao Paulo, Brazil ta birnin Addis Ababa.
Ya tashi ne a cikin jirgin Ethiopian Airlines.
Babafemi ya bayyana cewa wanda ake zargin yana ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 1.4 da aka boye a hannun jakunkunansa da kuma a saman jakunkunan.
Ya kara da cewa an kama matashin mai shekaru 33 dan asalin karamar hukumar Arochukwu da ke jihar Abia ne a ranar 26 ga watan Satumba, bayan jami’an yaki da muggan kwayoyi sun bankado inda ya boye haramatattun kayan .
“A yayin binciken farko, Okafor ya ce shi dan kwallon kafa ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Najeriya, Enugu FC, inda ya yi wasa har tsawon shekaru hudu kafin ya tafi Sri Lanka a shekarar 2014.
“Ya ce ya koma Brazil daga Sri Lanka bayan ya yi wasa na kaka biyu, amma bai iya ci gaba da buga kwallon kafa a Brazil ba saboda ba shi da takardu,” in ji Babafemi

Leave a Reply