Hukumar da ke yaki da masu safarar miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA, ta shafa fenti a jikin wasu gidaje shida da wani katafaren gini mai shaguna a Maiduguri mallakin jami’in dan sanda DCP Abba Kyari.
Fentin alama ce ana binciken gidajen.
Katafaren ginin bene ne mai hawa biyu mai suna Assurance Plaza da ke kan titin barikin Giwa a Maiduguri kuma yana da shaguna 100.
Baya ga ginin, hukumar na kuma binciken wasu gidajen zama shida a cikin unguwar masu hannu da shuni ta New GRA Maiduguri kamar yadda BBC ta kalato.
Wannan matakin na zuwa ne kasa da kwana biyu da NDLEA ta kama wani babban mai safarar Tramadol wanda darajarsa ta kai Naira biliyan 3, wanda hukumar ta ce yana da alaka da DCP Abba Kyarin.