Kwankwaso a ma’aunin adalci
Daga Datty Assalafy
dan ana batun ‘yan siyasa da suka cancanci su shugabanci talakawan Nigeria a sanina har yanzu banga wani ‘dan siyasa da cancantarsa ta kai ga na Kwankwaso ba
Tun dawowar Nigeria kan tsarin mulkin Demokaradiyyah ban san wani ‘dan siyasa da baya nuna kyamarsa ga talakawa kamar Kwankwaso ba, ban san wani dan siyasa da ya mayar da ‘ya’yan talakawa suka zama wani abu a duniya kamar Kwankwaso ba
Kai daga ganin tsarin Kwankwaso tun daga kan yanayin saka suturarsa da mu’amalarsa da kalaman bakinsa bawan Allah ne nagartacce masoyin talakawa
Abu daya yake cutar da siyasar Kwankwaso shine wasu daga cikin masoyansa suna da mummunan tarbiyya na zagi da cin mutunci, wato a fakaice yana da masoyan da amfaninsu bai wuce suyi zagi da tsinuwa ba, sai dai masu hankali a cikin masoyan sunfi yawa
Kamar kowani ‘dan adam shima Kwankwaso yana da nasa gazawar, sai dai alherinsa da kirkinsa da kaunarsa ga talakawa da aikinsa ya rinjayi gazawarsa
Allah Ka taimaki Kwankwaso