Jarumin fina-finan Hausa, furodusa kuma darekta, Bello Muhammad Bello, BMB, ya bayyana shirinsa na komawa sana’ar fim da kuma tambayoyi dangane da rayuwarsa, Daily Trust ta ruwaito.
A tattaunawar da aka yi da BMB, ya gabatar da kansa da farko.
A cewarsa sunansa Bello Muhammad Bello, amma an fi saninsa da General BMB. Furodusa ne shi, darekta ne, sannan kuma jarumi a masana’antar Kannywood.
Ya bayyana cewa ya na rubuta labarin fina-finai. Ya ce ya tashi ne tsundum a rayuwar musulunci a cikin garin Jos da ke Jihar Filato.
Ya ci gaba da cewa:
“Na yi makarantar firamare ta addinin musulunci inda na zarce Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Riyom.”
Ya ce ya zarce kasar Jamus inda ya yi karatun boko, daga nan ya wuce Belguim inda ya so zauna gaba daya.
Bayan an tambayeshi idan akwai abubuwan da ya yi wadanda daga baya a yi nadama a matsayinsa na jarumi, sai ya ce ya ce akwai.
“Maganar gaskiya akwai. Na yi danasanin shiga fadan Jarumi Ali Nuhu da Adam Zango. Na yi kuskure da na saurari bangare daya kuma na yi aiki da abinda na ji ba tare da na saurari dayan ba.
“Bayan na gane kuskurena na nemi yafiyar Ali Nuhu, shi da na yi wa laifi. Kuma yanzu haka mu na da alaka mai kyau tsakaninmu. Bayan nan mun ci gaba da abotarmu.”