Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya ce yana cike murnar samun labarin cewa har yanzu Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana nan daram a cikin Jam’iyyar PDP.
A cewarsa, “Na yi murna kasantuwar abokina Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa har yanzu shi ɗan Jam’iyyar PDP ne. Lallai ya yi abin da ya dace.
Na tattauna da wasu cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP daga Kano – waɗanda suka kawo min ziyara makon da ya gabata a gidana dake Abuja, ina da ƙarfin gwiwa cewa Sanata Kwankwaso da tawagarsa za su ci gaba da zama cikin jam’iyyar don mu gina tare da ceto Nijeriya.”