Sanatan Kano-ta-Kudu, Kabiru Ibrahim Gaya ya bayyana cewa ya rungumi ƙaddarar faɗuwa zaɓen Majalisar Dattawa na shiyyar Kano-ta-Kudu da aka gudanar, wanda Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP ya yi nasara.
Sanata Kabiru Gaya ya bayyana hakan ne cikin wani sakon murya da aka raba wa manema labarai a Kano a jiya litinin.
Kabiru Gaya ya kuma taya Kawu Sumaila murnar lashe zaɓen, tare da bashi tabbacin ba zai ƙalubalanci sakamakon zaɓen a kotu ba.
” Sau hudu na ci zaben sanatan Kano-ta-Kudu, shekaru 16 kenan. Kuma a cikin huɗun nan sau ɗaya kawai aka taba kai ni kara kotu sauran ukun ba’a kaini ba. Don haka ina sanar da Kawu Sumaila cewa ba zan kai shi kara kotu ba kuma ina taya shi murna,” in ji Sanata Kabiru Gaya kamar yadda muka kalato dag Daily Nigerian Hausa.
Sanata wanda ya yi Sanatan Kano-ta-Kudu sau hudu a jere, ya gode wa daukacin al’ummar yankin wadanda suka hadar da yan kasuwa, dattawa mata da matasa bisa hadin kan da su ka bashi tsawon shekaru 16.