BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Mutum 9 sun rasu bayan mota ta fada dam a Kano

Hukumar Kashe Gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane tara, yayin da aka ceto wasu uku a wani haɗarin mota da ya afku a dam ɗin Fada, hanyar Dayi a karamar hukumar Gwarzo ta jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Saminu Abdullahi ya raba wa manema labarai a yau Lahadi a Kano.

Ya ce haɗarin ya afku ne da yammacin jiya Asabar.

Abdullahi ya ce, “mun samu kiran gaggawa daga tashar mu da misalin karfe 06:45 na yamma, daga wani Ali Mai-faci, cewa wata motar Golf ta faɗa cikin Dam din Fada.

“Da samun rahoton, sai muka yi gaggawar aika tawagarmu ta ceto wurin da abin ya faru da misalin karfe 07:10 na yamma domin fito da wadanda abin ya shafa.

“Da isowarmu, sai muka gano cewa wata mota ce dauke da mutane kusan 12, kuma ba ta da lamba, ta taho daga Kano, ta nufi Katsina.

“Da kyakkyawan namijin kokarin mutanenmu da masunta na yankin, mun yi nasarar ceto mutane uku da ransu.

“An ceto mutane tara a sume kuma an kai su babban asibitin Gwarzo domin kula da lafiyarsu, yayin da likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwar wadanda abin ya shafa,” inji shi kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.

Abdullahi ya kuma bayyana cewa wadanda aka ceto ‘yan asalin jihar Katsina ne kuma duk wadanda ba a san sunayensu ba.

Leave a Reply