Labarai

Murtala Garo Na Qara Wa Gwamnatin Ganduje Karvuwa A Kano

Irin kulawa da xawainiyar da Kwamishinan ma’aikatar qananan hukumomi na jihar Kano Alhaji Murtala Sule Garo keyi na xawainiyar al’umma ta fannoni daban-daban na daxa qarawa tafiyar Gwamnatin Ganduje karbuwa a tsakanin al’ummar jihar kano. Jama’a da dama sun nuna cewa kwamishinan da ake ganin kusan duk a qunshin muqarraban Gwamnatin Ganduje babu wanda ya fishi kulawa da jawo wa Gwamnatin karvuwa sakamakon irin yadda yake sauraron jama’a da kuma tallafa wa buqatunsu baya ga kuma xinbin ayyuka da ma’aikatarsa take aiwatarwa da suke amfanar al’umma tun daga tushe. Wannan nema tasa jama’a suke masa kirari da  cewa yaqi saida kwamanda duba da yanda yake daxa samawa  tafiyar Gwamnatin  Gwamna Ganduje masoya ta  yanda ya zama kaifi xaya da dagewa kan ganin samun cimma  nasarar aiwatar da ayyukan da Gwamnatin  Ganduje take a lungu da saqon jihar nan. Alhaji Murtala Sule Garo shi ne kaxai Kwamishinan da idan aka je ofishinsa  zaka tarar da jama’a sun cika yana ganinsu haka ma gida kullum baka rasa shi da jama’a saboda yanda yake kulawa da girmam da mutunta mutane kullum. Wannan tasa Alhaji Murtala Sule Garo ya zama kwamishina da yake mutuqar samun girmamawa daga xinbin jama’a bama a cikin farfajiyar Jam’iyyarsa ta APC ba har waxanda basa tare a jam’iyyarsa saboda irin kyakkyawar mu’amalarsa ta girmamawa da mutunta al’umma da taimaka musu da yake a koyaushe. Ko wannan zave na fitar da Gwanin daya bai wa Gwamna Dakta Abdullahi Ganduje damar zama xan takara xaya tilo da rinjayen mutane kusan miliyan uku shi ya yi kai wa da kawowa a matsayinsa na babban jami’in zave daya lura da zaven na cikin gidan jam’iyyar APC na fitar da xan takarar Gwamna da aka yi.

Leave a Reply