BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Mun kashe ‘yan bindiga 30 da suka kai mana hari a Abuja – Sojin Najeriya

Aƙalla ‘yan bindiga da gwamnatin Najeriya ke kira ‘yan ta’adda 30 ne jami’an tsaro suka kashe a Abuja babban birnin ƙasar bayan sun kai hari kan rundunar tsaro ta fadar shugaban ƙasa, a cewar rundunar sojan ƙasar.

A ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka yi wa sojojin kwanton-ɓauna, inda kashe uku daga cikinsu tare da raunata wasu da dama lokacin da suke barin makarantar horon lauyoyi da ke yankin Bwari.

Da yake magana yayin wani taron manema labarai ranar Alhamis, shugaban sashen hulɗa da jama’a na rundunar, Manjo Janar Bernard Onyeuko, ya ce dakarun Bataliya ta 7 ne da Dakarun Musamman na 167 suka ƙaddamar da samamen tsakanin Lahadi zuwa Talata.

Ya ƙara da cewa dakarun sun yi nasarar kashe ‘yan bindigar a ƙauyukan Kawu da Ido ta hanyar tarwatsa sansanoninsu.

A cewarsa, dakarun sun ƙwato babur shida, da bindigar AK-47 biyu da sauransu a yayin samamen kamar yadda BBC ta ruwaito.

Leave a Reply