Al’ajabi, Kano Ayau Hausa

Miji Ya Yiwa Budurwarsa Kayan Sallah Matarsa Taje Ta Kwace Kayan A Jihar Kaduna

Wata matar aure taje gidansu budurwar mijinta inda ta dinga zazzaga tsiya har saida ta amso kayan sallah da mijinta ya dinkawa budurwar tasa.
Tace ta karbo kayanne saboda ya ki dinkama ‘ya’yanta da ita kanta kayan sallan, inda ta bayyana mana cewa ita bata damu ba da’ace ya dinkama ‘ya’yan nata guda uku amma ya ki yin hakan.
Sai dai majiyarmu ta samu tabbacin cewa mijin da kanshi ya shaidama matar tasa bashi da kudi, a dai bana zasu yi hakuri da ita da ‘ya’yan nata sai zuwa babbar sallah.
Kwatsam sai taji labari ya kashema budurwarsa kusan dubu talatin da biyar, su kuwa ya barsu ko takalmi bashi da niyyan saya masu.”
A nan dai ta tunzura ta tafi gidan su budurwar mijin nata data ji labarin irin abun da yayi mata suko ko oho.
Wannan lamari yafaru ne a wani gari da ake Kira da Kyamfa dake yankin ƙaramar hukumar igabi a jihar kaduna.

Leave a Reply