Kiwon Lafia

Mece ce tiyatar gyaran jiki?

Wane irin aikin tiyata akan yi a yanzu domin canja jikin mutane? Domin nakan ji ana cewa a yanzu za a iya canja wa mutum kamanni

Daga A.B. Misau

 

Amsa: Tiyatar gyaran jiki wadda a Ingilishi ake cewa Cosmetic Surgery a likitance kuma Plastic Surgery ita ce watakila kake nufi. Wato wannan tiyata tana nufin duk wata ’yar tiyata da za a yi domin yi wa jiki kwalliya ga mutum mai lafiya. A yanzu ana da jerin ire-iren tiyatar gyaran jiki da dama fiye da a kowane lokaci na baya. Misali, mutum mai gajeren hanci a dawo masa da shi dogo, kuma akan iya gyara wa karkataccen hanci, kamar wanda karan hancinsa ya karye a wani hadari; sukan iya rage fadin hancin idan ya yi fadi sosai, ko su kara fadin idan motsattse ne sosai. Haka mai gajeriyar haba za a iya dawo masa da ita doguwa; ko matar da fuskarta ta fara nuna alamun tsufa akwai allurar ‘mai-da-tsohuwa-yarinya’ mai washe kwalen tsufa. Ban da dashen suma da akan yi ga masu sanko akwai tiyatar kara tsayin wuya; haka sukan iya rage katon lebe, sukan rage tebar ciki da girman kirji ko ma su kara kirjin. Ga wadanda kunnuwansu suka fito tsaitsaye, su ma za a iya saisaita zamansu su dawo daidai. Kai har ragewa ko kara girman goshi ake yi.

Ita dai irin wannan tiyata ba wai ana yin ta don wani ciwo ba ne, don haka ba wani amfani za ta kara ga lafiya ba, irin wannan ce ma addini bai yarda da ita ba. To amma fa har-ila-yau akwai wata nau’in wannan tiyata wadda ita ma ta shafi gyara siffar jiki amma ga wadanda suka samu nakasa, wannan nau’i ne za a iya cewa ba laifi. Misali, mutumin da ya samu kuna a fuska fatar fuskar ta tattare, ana iya yado fatarsa ko ma namansa daga cinya a dasa a wurin da ya kone. Ko kuma wanda ya yi hadari ya samu karaya a hanci, za a iya gyara masa karayar. Wani lokaci akan iya sa wasu abubuwa kamar karafuna, ko robobi, da sauransu a wurin da ake so a gyara don sifar ta fito sosai.

 

Mene ne bambanci tsakanin kunnuwan dama da na hagu?

Daga N.I Batsari

 

Amsa: Duk yawanci sassan jikinmu masu wari da wari wato masu bangare bibbiyu dama da hagu idan ka lura ai za ka ga ba daidai da juna aka halicce su ba wajen siffa, a wani lokaci har da ma aiki. Misali karfin idonka na dama watakila ba lallai ba ne ya zo daya da na hagu. Don haka babu mamaki ka ga alamun bambancin siffa ko aiki a tsakanin su kunnuwanka. Amma hakan ba wai kuma yana nufin marar karfin yana da wata matsala ba ce. Idan kana zulumin wannan dan bambanci ko ciwo ne ko ba ciwo ba, za ka iya zuwa likita ya tabbatar maka. Misali akwai matsalar idon da za ta sa daya ya fi daya karfi, amma idan aka duba za a ga mai raunin yana bukatar gilashi.

 

Idan ina karatu da tocila da dare sai idona ya rika hawaye. Ko matsala ce haka?

Daga Umaru Sa’idu, Jema’a

 

Amsa: Eh, matsala ce wadda ke bukatar gwadawa da auna lafiyar ido a dakin aune-aune na likitan ido. Kuma watakila karfin hasken tocilar bai isa karatu ba, kuma ba daga sama yake zuwa ba, domin an fi son idan za a yi karatu hasken ya zo daga sama ba daga gefe ba.

 

Ko akwai taimakon gaggawa da za a iya ba wanda ya kone da ruwan guba na sinadarin acid?

Daga Ahmed Bichi

 

Amsa: Eh, hukumomin agajin gaggawa na duniya irin su Hukumar Red Crescent da ta Red Cross sun yi ittifaki cewa agajin gaggawa da za a fara ba wa wanda ya kone da gubar sinadarin acid kafin a rankaya asibiti ita ce ta saurin zuba ruwa a wurin na tsawon akalla mintuna 20, maimakon na a kalla mintuna 10 da akan yi wa kunar ruwan zafi ko na wuta. Da an gama wannan sai a yi maza a garzaya asibiti a duba wurin a san abin da ya kamata tun da wuri. Domin yawanci sinadaran acid ba kamar wuta ko ruwan zafi ba ne za su iya ci-gaba da cinye wurin da suka kona. Wato idan ana tunanin a fata ne kawai zai iya shiga ya fara cin har da naman karkashin fata, shi ya sa ma tun da fari aka ce a yi ta kwarara wa wurin ruwa kawai na tsawon akalla mintuna 20.

Ni kuma nakan samu matsalar ciwon ciki idan na ci abinci da dare, musamman tuwo. Ko bayan magariba ne sai na kai goman dare bai daina ba. Na je kyamis an ce ciwon olsa ne, shi ne nake neman shawara

Daga Fadimatu Mami

 

Amsa: Eh, akwai shawarwari kamar biyu. Shawara ta farko ita ce, to tunda kin je kyamis, su hasashen abin da suke ganin shi ne matsalar, sauranki asibiti inda za a duba ki a tabbatar ko haka ne ko a’a. Shawara ta biyu ita ce ta canja abincin daren zuwa mai ruwa-ruwa kamar fate wanda wadansu ke kira gwate, ko ma shayi da burodi kafin dai a gano ko mene ne a yi miki maganinsa.

Leave a Reply