BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Matsalar tsaro: Amurka ta gargadi ‘yan kasarta a Najeriya

Ofishin Jakadancin Amurka ya gargaɗi ƴan Kasar sa dake zaune a Najeriya dasu guji bin hanyar Jirgi dake Abuja.

Gargaɗin na zuwa ne bayan ƴan ta’adda sun kai hari a gidan yarin Kuje tare da sakin fursunoni a ranar Talata.

Haka zalika, Ƙasar Landan ta gargadi ƴan Kasar ta akan zuwa Jahohi 19 a Najeriya.

Daga cikin Jahohin akwai Borno, Yobe, da Adamawa, da Gombe, da Kaduna, da Katsina, da Zamfara, da Delta, da Bayelsa, da Rivers, da Akwa Ibom, gami da Jahar Cross River.

An shawarce su da suyi tafiya kaɗai a Bauchi, da Kano, da Jigawa, da Niger, da Sokoto, da Kogi a cikin kilomita 20 iyakar su da Niger a Jahar Kebbi, Abia, da Delta, da Bayelsa, da Rivers, da Plataeu da Taraba.

A cikin wata sanarwa da ofishin Jakadancin ya fitar, yace matsalar tsaro ta zama gagaruma a Najeriya.

Leave a Reply