Kano Ayau Hausa, Labarai

Matasan Kano Sun Kone A Daidaita Sahu Kan Zargin Kwacen Waya

Matasa sun kone wani babur mai kafa uku, wanda aka fi da A Daidaita Sahu, bisa zargin na masu kwacen waya ne a unguwar Kabuga da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano .

Fusatattun matasan sun dauki wannan mataki ne a daidai lokacin da wasu al’ummar jihar ke kiraye-kirayen a kafofin sada zumunta kan daukar mataki kan masu kwacen waya, saboda a yadda bata-garin suka addabi jama’ar jihar.

Kano na daga cikin jihohin Najeriya da suka yi kaurin suna wajen ayyukan masu kwacen waya ta hanyar amfani da makami.

Ko a makon jiya, sai da wasu masu kwacen waya suka caka wa wani matashi wuka suka kashe shi a Hauren Legal, kusa da Kwalejin Nazarin Aikin Shari’a na Aminu Kano.

Aminiya ta ruwaito yadda masu kwacen waya suka gota kashi bayan wata mata, suka kwace mata waya a unguwar Nassarawa da ke jihar.

A makon jiya ne dai rundunar ‘yan sandan jihar ta sanar cewa daga yanzu za ta rika gurfanar da masu kwacen waya a gaban kotu ne a matsayin ‘yan fashi da makami.

Masu kwacen waya sun yi ajalin mutane da dama, baya ga wadanda suka jikkata ko suka raba da dukiyoyinsu.

Leave a Reply