Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu tare da uwargidansa da dansa sun tsallake rijiya da baya yayin da aka kai masa hari a safiyar yau Talata a masaukinsa da ke unguwar Apo a Abuja.
Kakakin Ekweremadu, Uche Anichukwu ya ce, wasu mutane dauke da makamai sun kai hari gidan mataimakin shugaban majalisar inda suka yi yunkurin shiga gidan.
An kama daya daaga cikin wadanda suka kai harin yayin da sauran suka tsare. A yanzu haka wanda aka kama an mika shi ga hukumar ‘yan sanda