Mataimakin Gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna tare da sauran dubun dubatar ‘yan Jam’iyyar APC ne suka yiwa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari luguden kuri’u a zaben fidda gwani na shugaban kasa day a gudana a mazabar Gawuna dake karamar Huumar Nasarawa a Jihar Kano. Da yake zantawa da manema Labarai jim kadan da Kada Kuri’arsa Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya bayyana yadda zaben fidda gwamnin ya gudana cikin nasara da kwanciyar hankali,
Mataimakin Gwamnan na Kano Dakta Nasiru Gawuna ya kara da cewa tun daga lokacin da Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta yanke zabar amfani da salon zaben ta hanyar kato bayan kato Gwamnati ta maid a hankali wajen samar da dukkan abubuwan da ake bukata tare da wayar da kan al’umma. Dakta Nasiru Gawuna ya yi nuni cewa duk da yawan al’ummar Jihar Kano, al’ummar Kano sun tabbatar da matsayinsu na jama’a masu kishin Jihar Kano, musamman ‘yan Jam’iyyar APC wadanda kwarewarsu tayi fice a fadin kasar nan. Gawuna ya kara da cewa duk da yawan al’ummar Jihar Kano, acewar Mataimakin Gwamnan ya ce a tunanin sa a fadin kasarnan ba wata Jiha da zata nunawa Jihar Kano salon siyasa.
Saboda haka sai ya jinjinawa ‘yan Jam’iyyar mai albarka bisa zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari. Duk da cewa ba wanda ya tsaya takarar fidda gwani da Muhammadu Buhari sakamakon irin tabbacin da al’ummar kasa suke da shi kan shugaban Kasa Muhamamdu Buhari. Saboda haka Mataimakin Gwamnan Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai samu ruwan kuri’u idan a ka yi la’akari da irin ayyukan raya kasa da ake aiwatarwa a Jihar Kano.
Ya ci gaba da cewa Gwaman Ganduje ya samar da ayyukan raya kasa a cikin wadannan shekaru uku masu albarka, ya ce kuma alhamdulillahi muna yakinin idan al’umma suka sake baiwa Ganduje irin wannan dama zai samu damar ci gaba da wadannan ayyukan alhairi. Da yake tsokaci kan masu bukatar tsayawa takara mukamai daban-daban da suka shafi takarar kujerun Majalisun kasa dana jihohi na Jam’iyyar APC, Gawuna ya bayyana cewa duk wanda ya samu nasarar lashe zaben fidda Gwanin suna tabbacin samun hadin kai tare da goyon bayan ‘yan Jam’iyyar APC.
Saboda haka Gawuna ya bukaci masuirin waccan bukata da cewa su kudurce a cikin zuciyar su cewa kowannensu zai tafi ne akan tsarin Jam’iyyar APC. Saboda haka sai ya bukaci wadanda zasu fadi a zabunkan da ake shirin gudanarwa da cewa su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga Jam’iyya tare da karbar sakamakon zaben da kyakkyawar niyya tare da fatan alhairi.Hakazalika Dakta Gawuna ya hori Jama’ar Jihar Kano da su ci gaba da rungumar kaunar juna tare da kaucewa duk wani al’amari da zai rusa kimar Jihar Kano da kasa baki daya a zabe mai zuwa. Alokacin Zaben fidda gwanin Mataimakin Gwamna Gawuna na tare da shugaban kokas na karamar Hukumar Nasarawa, Alhaji Bala Usman, Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa kuma shugaban kungiyar shugabannin Kananan Hukumomi na Jihar Kano Alh. Lamin Sani da sauran masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Nasarawa. Kamar yadda Sakataren Yada Labaran Mataimakin Gwamna Malam Hassan Musa Fagge ya bayyanawa Jaridar LEADERSHIP A Yau.