A shekaranjiya Laraba ce jaridar The Sun ta Ingila ta ruwaito cewa mahukunta kulob din Manchester United da ke Ingila sun kakaba wa dan kwallon tsakiyarsu Paul Pogba takunkumin kada ya kuskura ya yi hira da manema labarai game da halin da kulob din yake ciki a halin yanzu na rashin kokari a kakar wasa ta bana.
Kulob din Manchester United dai ya yi wasanni hudu a jere ba tare da samun nasara ba. Na baya-bayan nan shi ne wanda kulob din ya yi kunnen doki da na Balencia da ke Sifen a ranar Talatar da ta wuce a gasar Zakarun Kulob na Turai.
Paul Pogba wanda ya samu sabani da koci Mourinho a makon jiya bayan ya soki kocin game da yadda yake tafiyar da harkokin kulob din, hakan ya sa kocin ya kwace mukamin mataimakin kyaftin daga wajen Pogba.
Wannan da wasu dalilai ne suka sanya bayan an tashi wasa a tsakanin kulob din United da Balencia sai mahukunta United suka fitar da sanarwar kakaba wa Paul Pogba takunkumin yin magana da manema labarai, kamar yadda jaridar ta ruwaito.
Paul Pogba dan shekara 25, rahotanni sun ce akwai yiwuwar ya bar kulob din United a kakar wasa ta bana ganin yadda kungiyoyin kwallon kafa da dama ciki har da na Paris Saint Germain (PSG) na Faransa suke zawarcinsa idan aka bude kasuwar cinikin ’yan kwallo a watan Janairun 2019.